Shin Menene Blog ?
Blog Wani Karamin Shafi Ne Da Ake Budeshi A Internet Domin Bayyana Abubuwa Dayawa Kamar Koyarwa, Wakoki, Videos, Labarai, Kokuma Yadda Za A gwada Maka Yadda Zaka Bude Naka Blog Din Wannan Shine.
Shin Menene Website ?
Website Shima Kamar Blog Yake Amma Gaskiya Akwai Banbanci Domin Shi Website Ana Budeshi Ne Domin Wata Kungiya Su bayyana Manufofinsu Ko Ayyukansu To Amma Idan Za Ai Kudin Goro Da Blog Da Website Duk Abu Dayane Wannan Shine.
Mecece Blogger.Com ?
Blogger.Com Wani Website Da Aka Bude Shi Domin Bawa Mutane Dama Su Bude Karamin Blog Ko Website Domin Bayyana Baiwar Da Allah Yaimusu Blogger Yakai Sama Da Shekara Ashirin (20) Da Kirkira A Duniya Kamar Yadda Nima Zan Nuna Muku Yadda Zaku Bude Naku Blog Kubiyoni.
Abubuwan Daza Kabukata Kafin Kabude Blog ,
Gmail Account Ko Yahoo Account
Laptop Ko Wayar Android 📱
Chrome Browser Ko Firefox Browser
Yanzu Zamu Tafi Kaitsaye Yadda Daza Kubude Blog Dinku.
Idan Kabude Browser Dinka To Kawai Karubuta Blogger.com Ko Kuma Kashiga Ta Nan Blogger.com Zaka GA Shafi Kamar Wannan.
Idan Wannan Shafi Ya Bayyana Abinda Zakayi Anan Kawai Shine Kadanna Inda Nasa Kibiya Wato " SIGN IN " kana Dannawa Shafi Nagaba Zai Bayyana Kamar Haka.
Anan Zakayi Sign in Kamar Yadda Nagaya Abaya Katabbatar Kana Da Gmail Account To Anan Zaka Saka Gmail Dinka Idan Kasa Sai Kadanna "Next " Zai Nuna Maka Inda Zaka Saka PASSWORD Din Gmail Dinka Kana Wucewa Nan Zaka Iya Ganin Shafi Kamar Wannan.
Abu Daya Zakayi Anan Kadanna Inda Aka Rubuta "Create Blog " Nayi Alama Da Kibiya Agurin Yanzu Muje Gaba.
Wannan Shafi Yana Da Muhimmamci Sosai Don Haka Kakula Nayi Alama 1 2 3 Alama Tafarko Wato 1 Shine Title Maana TAKE Anan Zaka Sawa Website dinka Suna Misali HAUSA TECHS Zaka Iya Rubuta Wanda Ranka Yakeso.
Alama Tabiyu Wato 2 Shine Address Wannan Shine Zaizama URL Na Website Dinka Misali Inaso Nabude Blog Da Suna Hausatechs Idan Nasaka Sunan Zaizama Hausatechs.blogspot.com Kuma Kakula Zaka Iya Sa Sunan Dakakeso Sucema Baka Dadamar Mallakarsa Kodai Wani Yarigaka Kokuma Bazaka Samu Damar Mallakarsa Awannan Lokaci Ba.
Yanzu Misali Munsa Sunan Blog Da muke Budewa Hausatechs.blogspot.com Abin Tambaya Shine Tayaya Zai Koma Hausatechs.com To Amsa Itace Ita Wannan .Com Siyanta Akeyi Idan Kasaya Sai Kacire Blogspot.com Blog Dinka Zaikoma hausatechs.com Yawwa Yafi Dadin Rubutawa Yanzu .
Idan Kagama Zabar Sunan Blog Dinka Akasa Zaka Ga Wasu Hotuna Wadannan Sune Themes Wato Dizayin Sune Zasu Haska Blog Dinka Kuma Su Kawatashi Kazabi Wanda Yafi Burgeka Idan Kagama Sai Kaddanna Inda Nayi Alama Da 3 Wato Create Blog Shikenan Kabude Blog Naka Nakanka. Yanzu Sai Me ?
Akwai Abubuwa Dayawa Domin Yanzu Aka Fara Aikin Nikuma Hannuna Yagaji Da Rubutu Don Haka Sai Muhadu A Post Nagaba Inda Zamuyi Bayani Daya Bayan Daya Akan Wadannan Abubuwa:-
1- Post Shine Gurin Rubuta Aduk Lokacin Da Kakeson Yin Bayani Akan Wani Abu Misali Kamar Wannan Wanda Kake Karantawa Yanzu.
2- Stats Shikuma Gurine Dazai Nunama Tarihin Wanda Suka Shiga Blog Dinka Sannan Daga Ina Suka Shigo Duk Zaka Sani.
3- Comments Wannan Gurine Na Korafi Wadanda Suke Shiga Website Dinka Idan Suka Ga Wani Abu Dasuke Bukatar Tsokaci To Zasu Iya Fadar Abin Daya Shige Musu Duhu Ko Shawara Tahanyar Comments Kuma Kaima Zaka Iya Bada Amsa Kokuma Karin Bayani .
4- Earning Shi Kuma Gurine Nasamun Kudi Wato Duk Lokacin Da Blog Yakai Matakin Samun Kudi To Tahanyar Earning Zakayi Register Domin Fara Samun Kudi.
5- Pages Sunansu Peji Anan Zaka Iya Bude Kowane Peji Kake Bukata Kuma Suna Da Matukar Amfani Dasune Zaka Iya Samun Damar Register Domin Samun Kudi Kamar Yadda Nafada Abaya.
6- Layout Wannan Shine Gurin Gyara Dizayin Kacire Wani Abu Kokuma Kakara Kokuma Ka Chanzawa Abu Gurin Zama Duk Zaka Iya Da Layout.
7- Theme Wannan Shine Dizayin Anan Zaka Shiga Idan Kana So Kachanza Dizayin Kokuma Kayi Gyare Gyare Amma Akwai Abubuwa Daya Kunsa Dayawa Ahankali Zamuyi Bayani.
8- Settings Wannan Shima Gurin Gyara Ne Amma Da Bambamci Dana Baya Akwai Abubuwa A Settings Wanda Anan Gaba Kadan Zaku Sani.
Domin Karin Bayani Kokuma Kuna Son Mallakar Blog Kamar Hausatechs.Com Kuturo Sakon Watsapp Ta Wannan Number 07066870719
0 Comments Yadda Zaka Bude Free Website Ko Blog A Blogger.Com In (2019) HausaTechs.Com
Tags Blogger.Com
Yadda Zaka Bude Website
      
 NEWER
Yadda Zaka Aika Application Daga Watsapp Zuwa Ko ina Da File Explorer App ¦| HausaTechs.Com  OLDER
Yadda Zaka Bude Free Website Ko Blog A Blogger.Com In (2019) HausaTechs.Com
YOU MAY LIKE THESE POSTS
April 09, 2019 Yadda Zaka Bude Page A Blogger | Hausatechs.com
March 26, 2019 Yadda Zaka Bude Zip File Wato Extract Da Zip Extractor App A Wayar Android
March 26, 2019 (Complete Guide) Yadda Zaka Dora Template A Blogger | Hausatechs.Com
POST A COMMENT
Search SEARCH THIS BLOG
FOLLOW BY EMAIL
Get all latest content delivered straight to your inbox.
SUBSCRIBE
February 03, 2019
February 08, 2019
April 15, 2019
April 09, 2019
April 10, 2019
April 15, 2019
April 10, 2019 Yadda Zaka Bude Free