Ummanta tana zaune tana tace gasarar
Wacce aka kira da Umma ce ta daure fuska ke jarababbiya sauraramin,niba uwarki bace zaki dinga gaya min magana inda kika ga dama?,ko ni sa'ar ubankice,har ni zakiyiwa wa'azi kamar kanwar uwarki,sai da safe ki taso sakalo sakalo na sammiki koko,kin dauki aikin banza a kanki,kin rasa me sonki tallanma kinki yi kince ke boko zakiyi ayi mugani ai duniya ce,
Haba Umma daga cewa kiyi sallah shine kike min baki?kin San ma'anar duniya ce,ku gidan nan Baku da aiki sai zage zage,duk kun gama kwashe mana Albarka,taya zamu samu miji,kuma boko tun daga primary waye yake daukan nauyina?itacen kara nake yowa a kauyen nan haka gashi har ina ss2,ai abin ku jinjina minne amm kullum kunfi so kuga na shiga duniya dan na samo muku kudi haba Umma,ya kike haka ai gwara idan bake kika haifeni ba ki fada min nasan matsayana tun wuri.
Ke tashi ki bani waje jakar banza.wani bakin cikine ya cika zuciyar Amana,Sam basuyi dacen iyaye ba,yo ni da za a dinga min fada wani ciyar dani akeyi?sutura ake min ko sabulun wanki bare na wanka ba ayi mana a gidan nan,kuma sai a bimu da zagi nifa bazan dauka ba cewar Amana tare da ficewa daga gidan.
kowa a gidansu babu na gari a cikinsu,gaskiya Allah kawo min sanadiyar tafiya Cirani na yi wajen kudu,na huta kawai da bala'in gidan nan,Allah sa Baba ya turani cirani nima irin su Hamza na tafi na huta da masifar gidan nan.
Wannan wanne gidane kenan,da alama babu me tarbiyya a gidan kaf. bari muji tarihinsa.
GIDAN BAKI kenan gidane Wanda me Gidan yake saukar mutane Baki idan sunzo gari suna Neman masauki sai ya saukesu amma iya mata banda maza,baya saukar maza a gidansa,shine dalilin da ake kiran da gidan Gidan Baki.
Gidane Wanda yake cike Da mata da maza.da yan gidan da kuma baki iya mata amma.
Baba me gidan shine Sulemanu Harka dan Asalin kauyen Albasune LGA ne dake Kano state,Amma aikin gini yasa ya koma garin Wudil da zama,Babar Sulemanu Harka wato Ille ta haifi yara kanne da Yayyen Sulemanu harka amma duk su nutsatsune suna zaune a can kauyen Albasu lafiya da iyalensu yayinda Sulemanu ya dauke Uwarsu wato Ille,saboda tana sana'ar soya kosai sai wayo yake mata tana ciyar masa gida da kudin da take nema,.
Ille ita kanta tasan Sulemanu Harka ba mutumin kirki bane amma ba yanda ta iya dashi,haka take Sana'a tana ciyar masa da iyalensa,
Sulemanu Harka matansa 4 Haule itace ta farko ana ce mata Goggo,yaranta 10 Maza 4 mata 6 Safiyya itace Babar Amana suna kiranta Umma, yaranta Uku maza 2 mace 1 Amana.
Laure Hajiya kenan ta uku yaranta 5 Maza 3mata ,
Sai Raliya Amarya tana da yara 8 maza manya 4 sai mata ma 4.gaba daya yaransa 25 kusan mata 4 kacal akayiwa aure, matan suna gidajen mazajensu a kauyen Albasu wasu a garin Albasun,
Saura mata da yawa suna a gidan ciki harda Amana,maza kuwa ba wanda yayi aure cikinsu kawai iya shege sukeyi a garin, Sulemanu Harka sana'ar gini yakeyi sosai tun yana da kuriciya har ya girma yayi yara magina.baya taimakawa iyalansa da kwandala sai matan banza,Sai kuma yaci me kyau a waje yasha me kyau,ga sutura me kyau,sai ka Rantse Sulemanu ba a gidan kasa yake kwana ba,
Yaransa duk ba munana suna da kyansu,Amana tafi kowa kyau a gidan sai dai wasu su fita haske shima da kadan don itama fara ce Amana.
Talakane na karshen karshe,saboda ko ya samu baya tsinana komai ga iyalinsa,sai dai yaci tsire da kudin,domin kullum yana gaban tukubar me nama,gidansa kuwa ko masara ya kasa siya musu ko wacce Sana'a takeyi tana ci da kanta da yaranta,Sulemanu Harka gawurtaccen dan Neman matane,kaf kauyen da wasu garuruwan sun sanshi,shi yasa idan yaji baki mata to shi zai basu masauki yana zagawa wajensu.
Bashi da Amana,ko yarinya ka kawota gidansa riko sai ya ci amana ya lalata ta karfi,haka baki wasu su gudu wasu su tsaya su sha harka,yaransa ma sunsha kama Baba da mata,matansa har fakonsa sukeyi idan dare yayi,sabo da ko yar uwar matansa ne sukazo sai ya zaga wajensu ya kwashi Harka,
Bashi da abokin da ya wuce limamin garin domin halinsu daya,
Sulemanu Harka ko yarsa kaje nema idan baka da kudi to bazai baka yarsa ba,kuma idan kana zuwa zance wurin yarsa to sai ya dinga rokonka kudi,haka gaba daya sai Allah ya bashi yara gaba daya tantirai,Amana ce ta gari a hakan lol kaf gidan babu me nutsuwar Amana a hakan.
Mazan gaba daya wasu barayine,wasu yan wiwi,wasu yan Neman mata, domin suma suna lallabawa wajen baki masu sauka,na gidan aure ma ko wacce da rashin mutuncin da take shukawa a gidan mijinta,kullum a kawo kara da Sulhun yaran Sulemanu Harka ake,babu na ciki babu ga na wajen,kowa da halinsa,
Su Kansu yaran sun San basuyi dacen iyaye ba,su kuma iyayensu mata matsalarsu rowa, zagi da tsinuwa kala kala,sun gama raina mijinsu saboda ya zubar da mutuncinsa.a cikin labari zaku ci gaba da jin Halin kowa a Gidan Baki.
Amana kyakyawar yarinyace ta kwatance fara ce Amma ba kar ba,doguwace ga shape,duk inda kake neman diri to kazo wajen Amana, shekarunta 18 going to 19, gashine da ita ya wuce kafada kadan baki wuluk,gata da idanu dara dara masu tsananin kyau,gashin gira dumbul dashi,dan bakin nan cut,lips light pink,hancinta dan dai dai bai cika tsini ba kuma ba gajere ba,ga dimple idan tana magana bare tazo yin dariya,hakora yar yar dasu kar kar,saboda kullum cikin yin aswaki take ko yaushe,skin dinta me laushin gaske, gata da tsafta ba laifi.
Amana yarinyace me son al'adun maza,haka take tun tana karama rayuwarta da maza takeyi,shi yasa kaf garin wudil bata da kawa mace ko daya, sai Maza,bata da mutunci ko kadan idan ka shiga safgarta,ko uban waye komai girmansa,macece me karfi da zafin nama,ga juriya da taurin rai,idan fada ya hadaku tofa sai dai a mutu bata ji ba ta gani,idan ta fara dukan mutum sai ta gaji da kanta,kowa daya Santa tsoronta akeji ko a gidansu Amana sarauniyace dan ko waye bai is a ba,iyayenta kawai take dagawa kafa,
Ba wani abu na nafeela takeyi ba amma duk farilla tana cikawa,Sallah bata wuceta duk inda take,gata da son ilmi,gidansu ba a sasu a islamiyya bare boko amma har gona take zuwa tayo ciyawa ko kara ts siyar ta sayi littafan schl,haka ta gama primary yanzu tana ss2 a wata government schl ta garin,duk da ba wani turanci ta iya ba amma tana iya karantawa,haka islamiyya ma,tana da haddar izu 30 ga wasu littatafan tayi,duk gidan ita kadaice take zuwa schl,har yaran gidan sabo da tsoron Amana da sukeji take korasu makarantar Allo dolensu suke zuwa,
Kuma idan baka kawo mata haddar karatun ba sai ta farfasawa yaro jiki,ba ruwanta don kaninta har kashi ta tsaga masa garin duka bai iya karatu ba,har yayyenta tsoronta sukeyi sun san karfin Amana,ba mutunci ba daga kafa,shi yasa a gidan ita kadai ce take sa doka kuma dole abi dokar,
duk masifar Amana bata yi a schl tunda wani malami ya kusa korarta daga schl din gaba daya sai ta daina komai da take musu,sai kadan kadan takeyi, domin tunda ta fara schl take jibgar dalibai,tare da karya kafafun yaran mutane,domin har malami cin kwalarsa takeyi ta fesa masa mari,
Gata da kokari da tsafta,shi yasa aka bata head girl,tunda aka bata mukami idan yaro yayi late sukaganta a gate juyawa sukeyi gida sabo da sun San dole sai ta fasa ma jiki,ta gagari malaman bare abi wa yaro hakkinsa,
Amana yar rigima ce sosai,tunda aka haifeta Ummanta ta zabi wannan suna Amana aka radawa yarta,wajen aiki kuwa ta iya girki kala kala domin Amana har wajen wata Bilkisa me tuwo tuwo take zuwa tana tayata girki ta bata kudi,dasu take biyan bukatunta da dama,
Amana Ummanta bata da halin kirki,ga son kudi,bata iya taimakawa yaranta da ko kwandala,kowa yaro da babba dake gidan Sulemanu Harka Neman na kansa yakeyi,kowa ta kansa yakeyi babu me taimakon wani da ko kwandala,gwara Amana tana bawa babanta wani abun idan ya rasa,har su Hamza takan sai musu kokon safe watarana,sabo da Amana ta fisu zafin nema,ba ruwanta kullum cikin Neman hanyar samu take,kuma in taje neman aiki wajenka tofa dole ne ka bata aiki tayi ma,kuma sai ka biyata dai dai da guminta, sauran yan matan da basuyi aure ba maza suke damfara da yaudara su sami kudin sabulu da sauran kayan sawa,shi yasa suka fi Amana sutura da yawa,sabo da Amana bata da saurayi sai abokai,bata da kayan sawa,atamfarta kodaddu kala 2ne sai tsimmokaran da take sawa,suma wasu wandon duk na su Hamza ne da kannenta,take dauka idan zasu jefar sai ta karba ta wanke taci gaba da sawa tana hadawa da rigar atamfa,Ummanta tana Sana'a tana samun kudi amma sisi bata iya bawa Amana,hatta kokon Safe sai dai Amana ta siya, idan ba kudi ta tafi wajen abokanta maza ta samu,amma tana bawa kannen Amana Maza,basa shiri da Amana da Ummanta sabo da Umman Amana tafiso Amana ta dinga damfarar maza tana samo musu kudi,amma Amana taki yarda kuma bata da me sonta.
Shi yasa Amana tace abokai maza sunfi mata muhimmanci,ga kyauta,gashi basu fiye gulma da hassada irin ta mata ba,Namiji ko ya kuke mutunci zaka moreshi,sabanin mata da yawa sai su dinga yi ma hassada ma,idan sunga ka fisu sai gulma da bakin ciki.
Yawan Hulda da Maza yasa Amana takeyin acting din maza, sauran yan uwanta duk Suna Neman mata,matan ma sabo da son kudi Neman maza sukeyi,Amana ce kadai cikinsu Bata ma da saurayi bare ma ya taba jikinta,kuma mazan da take Hulda dasu tsoron jarabar Amana sukeyi ko yatsanta basa rikewa.
0 Comments