https://lucsontech.blogspot.com/?m=1
Assalamu Alaikum yan uwa barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha, a makon daya gabata nayi jawabi filla filla matakan da za’abi wajen bude blog tare da blogger a wannan karnin kuma insha Allahu zanyi bayanine yadda ake saka rubutu (posting) a shi blogger wanda hakan yakan baiwa maziyarta shafinka damar karanta wannan rubutun.
Abu na fari da mutum zai fara anan shine shiga account dinsa domin kuwa ba yadda za’a yi mutum yasa wani rubutu a shafinsa ba tare da ya shiga account dinsa ba a rubutun daya gabata nayi jawabi dalla dalla Yadda ake shiga account wato login a blogger, sannan kuma bazai iya sa wani abu ta hanyar ziyartan shafinsa ba misali in addreshin shafina duniyanfasaha.guidetricks.com shiga wannan addreshin kawai zai bani damar karanta abinda aka sanya ne; in har mutum yana so ya saka rubutu to dole sai yabi matakan da zan zayyano.
Idan mutum yana so yayi post a shafinsa na blogger a daidai hannunsa na hagu bayan yashiga wato login a account nasa sai ya latsa inda aka rubuta Post na fari zai kaisa izuwa nan.
Za’a tatar da karamin akwati na fari ana kiransa title a turance shine inda mutum zai rubuta suna ko silar abinda yake son rubutawa misali anan sunan wannan post din “yadda ake post a blogger” sai mutum ya sanya ta a daidai wajen.
Babbar nan kuma shine wajen da za’a saka duk jawaban da ake son nunawa karkashin suna da aka sa misali duk wannan dogon surutan nawan suna cikin wannan babbar akwatinne amma shi asalin suna silar wannan rubutun na Yadda ake post a blogger yana cikin akwatin na fari ne. haka zalika mutum zai iya cope abu daga wani dandalin sadarwa kamar su whatsapp ko kuma facebook sannan yayi pesting nasa kamar yadda akeyi a wajajen da aka copo abun (ta hanyar latsawa a tsaya nayan wasu dakikai sannan na danna ma bullin “paste”). Bayan mutum ya kammala sai ya latsa ma bullin “publish” wanda ke rubuce a sama a daidai hanunsa na dama domin fitar abinda ya rubuta a shafinsa.
Yana da kyau mutum ya kula da wayannan madannan guda hudu wanda suke sama a hannun dama wato “publish”, “Save”, “Preview” da kuma “Close” akwai banbanci sosai tsakanin wayannan madannan.
Abu na fari wato publish amfaninsa shine duk sa’in da ka latsa wannan mabullin to duk abinda ka rubuta zai fito a shafinka wanda duk ya ziyarci shafinka zai gani sannan kuma zai iya karantawa. Abu na biyu kuma a jerin madannan shine “save” amfanin wannan mabullin shine misali ina rubutu yanzu sai wani matsala ya taso wanda ya zamana dole ne na bar abinda nakeyi na je izuwa ga shi to mutum sai ya latsa wannan mabullin wanda duk sa’in da ya dawo zai sami abinda ya rubuta yadda yake sai dai akwai banbanci tsakanin sa da wanda nayi bayani a baya wato publish shi save in ka latsa sa ba zai fito a shafinka ba ma’ana ko mutum ya ziyarci shafinka bazai gani ba amma kuma kai ko wani sa’in ka dawo admin dashboard naka zaka tarar da abinda kayi saving nasa yana nan daram sai dai in ka goge (wato kai daya ne zaka iya ganin yayin da kayi saving).
Na uku kuma shine “preview” wannan mabullin amfaninsa shine zai baka damar ganin yadda abinda ka rubuta zai fito a shafinka kama daga surar rubutun da kuma tsari. Abu na karshe kuma a jerin mabullan shine “close” amfanin sa shine cirewa ko kuma koma wa baya ba tare da ya adana ba amma wasu sai’in yakan iya adanashi wato auto saving a turance sabida duk lokacin da kake rubuta wani abu a wajen abar rubutun yana adanashi sabida gugewa wata matsala irinsu daukewar wuta ko kuma daukewar layin sadawar wanda koda hakan ya faru zaka samesu yadda suke ba tare da ka sake wani sabon aiki ba.
Wannan shine takaitacciyar bayani yadda ake saka rubuta a shafin blogger. Ku kasance tare da Duniyan Fasaha domin samun ingattaciyar abubuwa wanda zasu taimakeku a harkokin yau da kullum naku a koda yaushe Jikan marubuta kuma sharif
0 Comments