Bafulatana taje ta sauke kwaryar nonon a gaban wannan matar, sai bayan ta ajiye sai taga ashe mahaukaciyace, ga kuma wata katuwar sanda akusa da ita sai zare idanu take babu alamun sauki a tare da ita.
Cikin tsawa mahaukaciyar tace da Bafulatana "nawa-nawa?"
Jiki na rawa bafulatana tace "kona nawa kikeso ai sai a baki ".
Mahaukaciya tace "To auno na naira."
cikin rawar jiki Bafulatana ta auno dayawa sai tace mata gashi. Sai ta sake daka mata tsawa tace "Kyauto!"
Bafulatana ta sake kamfatowa ta zuba, sai gogar tace mata "To shanye!" Bafulatana ta dauka ta shanye.
Mahaukaciya ta kara cewa kara aunowa, ta kuma cewa ta kyauta, ta kara zubawa sannan ta kuma cewa ta shanye.
Bafulatana ta kuma dauka ta kuma shanyewa Mahaukaciya ta kara cewa ta auno a karo na uku. Sai shima ta shanye daga nan kuma sai ta daka mata tsawa tace "Yan banza, ashe kuna so kuke kaiwa kasuwa? " Tashi ki bani guri. Bafulatana ta suri kwarya ta hanzarta barin gurin.
To wannan shine asalin karin maganar da ake cewa "ANASO ANA KAIWA KASUWA.
Domin samun sauran labarun musha daria shiga nan
👇👇👇
0 Comments