Sanye take cikin wata jemammiyar rigar atamfa ko kugu bata kai ba,ga wani wandon yadi ja ajijinta dogo,ta nannade kafa daya iya gwiwarta,wata dagargajajjiyar p cap ce a kanta,tafiya take tana bouncing har wani dinginsa kafa daya takeyi,irin tafiyar nigogi maza takeyi tana shan kamshi tare da dauke kai sama tana hura hanci,tafiya takeyi tare da sa hannayenta a aljihunta tana bouncing tare da yin doro tana kwobarewa hadi da budawa.

     Bata kula kowa kawai kwana take sha,wata dandazon majalisa ta maza tazo,tana zuwa aka fara ihu da tafi sai Amana,kallonsu tayi tare da kara kwobarewa tace sai Baba,sa'a dai sa'a dai tayi Gaba bata kara yin magana ba tafiya kawai takeyi,wani yaro taci karo dashi,sai da ya buya a lungu yace Maza Mazaje Cike da bala'i ta dago kanta aifa sai  ta hango yaron,da gudu yaron ya zura,ta bishi itama sai da ta kure masa gudu har cikin gidansu yaron ta kamoshi a gaban Uwarsa ta hau jibgarsa kamar Allah ya aikota,mutane sun taru amma ba Wanda ya riketa saboda kowa yasan halinta,in tayi fushi ba a iya tsaidata,suna ji suna gani ta farfasawa yaron nan jiki sannan ta gyara p cap dinta sosai ta da kyar take gani tsabar janyo hular da tayi, gaba tayi tare da bouncing,ta kusa zuwa kofar fita daga gidan tayi tsalle tayi ball da wani baho da ta gani a hanyar kofar fita daga gidan sai da bahon yayi raga raga,sai da ta fita ta bar gidan sannan mutane suka sami bakin tsine mata tare da Allah wadai da zuriyar Gidan baki gaba dayansu,kowa da abinda yake fada akan wannan matashiya da sauran yan uwata tare da iyayensu.

      Har kofar wani gidan kasa tazo kato da alama shine gidansu,Babanta ta gani a waje tare da mutane a kofar gidan Sallama tayi musu tare da cewa Allah barmana Baba,sai me gida wlh,tayi cikin gida,da wani gurjejen namiji ta hadu da gani katon dan Wiwi ne,lips dinsa sun nuna da tafin hannunsa,cije baki yayi tare da karkace shi gefe,ke dan Uwarki daga Ina haka?hannayenta biyu a Aljihunta tana hura hanci tare da ja baya,ta kara yin doro tace kafa ja girmanka Hamza,dan zan iya takeshi kasan da wa kake magana dan tsab zan Zagi Amarya uwarka,kasan Halina ko?

      Jinjina kai Hamza yayi tare da cewa zan tattakaki in bakiyi hankali ba,bani da mutunci,to ni din an fada ma mutuncin gareni cewar Wacce aka Kira da Amana.tsaki taja tare da banke Hamza tayi cikin gida,tana shiga Ashar ce take tashi a gidan ana ta dambe tsakanin yan mata gidan,
     Iyayensu ma sai dirko ashar sukewa junansu,ruwan Ashariya kala kala ce ke tashi a gidan,nan take ran Amana ya baci ko kallonsu batayi ba ta wuce cikin dagargajejen dakinsu,Wanda yake daf da ruftowa.

     Sallamar megidan sukaji da alama shine babansu,shima Ashariya ya Shiga dannawa yaran tare da iyayen su hade da kallon wata yar yarinya bata wuce 7yrs tana gatsine da harara  yace tafi can shegiya da kai kamar kuda,kallon sauran matan nasa yayi da yaransa maza da mata yace wacce bata fasa ba taci ubanta shegu tsinannu,tambadaddu,bakin da aka sauka a gidan ne suka fito daga masaukin da aka basu suna bada hakuri,
  Matan ne sukayo kan bakin da masifa kamar zasu cinyesu da zagi na tashin hankali.

    Me gidan ne yayi tsalle ya dire yace kar tsinanniyar data kara zagar min bakina,bakin Alkhairi,dole kuma na dinga saukar baki a gidana,wlh babu yar wata katuwa da ta isa ta taka min birki.
     Wata ce a cikin matan nasa tace tambadadden dan iska dama dole kace haka munafuki,Allah ya isa duk ka tarwatsa mana yara,ka lalatasu,dayar ma tace an dai ji kunya kwarton Banza,wata tsohuwa ce tukuf itama ta fito tana ba kwarto bane yaro na,kar ku kara zagar min da shegu jarababbu,haihuwar Asara.
   Watace ta zaburo itama a cikin matan ta nuna me gidan,tace ga tsohon haihuwar asara kwarto maci amana.Amana ce ta fito daga dakin tana budawa tare yiwa mutan gidan kallon banza,tace kuna yawa fa,kuna da matsala,dan Allah ku rufe mana baki wlh ko yanzu ayi abin kunya a nan wajen nan ko Baku gane bane eh?
 
      Me gidan yace yawa Yar Amanata kiyi maganinsu,sai Baba  kaima fa Baba kana da Matsala fa,ka dinga kiyayewa duk kabi ka jona mana masifa da irin abinda kakeyi a gari.
 
    Baba ne ya kalleta zaki ci Ubanki kema shegiya me suffar maza,jibi yanda kikeyi, wa zaki samu ya aureki haka? Shi yasa baki da mashinshini,kinyi kwantai anyiwa kannenki aure ke kina shirme a gari,
      Cike da takaici ta kalli kanta tare da sa hannu daya a Aljihu tare da cewa Baba ni ba gudun maganarka nakeyi ba,bana tsoronku ku kanku kun sani,kawai biyayya nake ma amma dole a fadama gaskiya ka gane Tsoho kana yawa wlh,wannan abin da kakeyi ba me kyau bane,shi yasa muka lalace,dole na fada ma gaskiya,ka gyara badan mu ba ko dan Allah kaji tsoronsa.
  Rufe min baki shashasha ubanki nakeyi? Hmmm Allah baka Hakuri Baba nasan yanzu zaka iya tsine min.
     Ta inda kikafi yan uwanki hankali kenan akwai biyayya ga iyaye,ga sallah akan lokaci,cewar Baba Dariya amana tayi kadan tare da fadin Allah barmana Baba,ammafa Baba Allah shirya mana kai.ki kiyayeni Amana cewar Baba,sorry Baba Amana ta fadi,
    Baba yau ba dan tsire ne?cewar Amana, Babane ya watsa mata harara tare da cewa ubanwa zai sai miki tsire maganin me kike min a gidan nan,ke ba saurayi ba  bare nasa rai zan samu kudi,tafi kiban waje shashasha.bouncing ta kama yi tare da kwobarewa tana kunkuni,wofi banza da baki kamar gidan tsutsa cewar Baffa.Anayin kiran sallar Magriba Amanace ta Riga kowa yin amana
a da Sallah a gidan.


Kubiyo mu a shiri nagaba don cigan littafin mu
Mai suna ciranin amana
Idan kunji dadin littafin se kuyi mana comment